Ehlibeyt (as) Haber Ajansı ABNA - Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibuf ya bayyana cewa siyasar juyin juya halin msulunci a nan kasar Iran ta sami tsayawa a gaban tsarin jari hujja wanda ya mamaye duniya, sannan Karin karfin tsaron kasar sun hana makiya tabata.
Tashar talabijin ta Almayadeen a kasar Lebanon ta nakalto shugaban majalisar yana fadar haka a safiyar yau Lahadi a zaman majalisar dokokin kasar a nan Tehran.
Shugaban majalisar ya kara da cewa majalisa da 11 wacce yake jagoranta zata bi tafarkin fuskantar kasar Amurka da kuma neman daukar fansar kisan shahid Qasim Sulaimani.
A ranar 28 ga watan Mayu mai karewa ne aka zabi Muhammad Bakir Qalibuf a matsayin shugaban majalisar shora Islami ta 11, a nan kasar Iran.
/129
1 Yuni 2020 - 07:35
Lambar labari: 1042209
Shugaban majalisar dokokin kasar Iran Mohammad Baqir Qalibuf ya bayyana cewa siyasar juyin juya halin msulunci a nan kasar Iran ta sami tsayawa a gaban tsarin jari hujja wanda ya mamaye duniya, sannan Karin karfin tsaron kasar sun hana makiya tabata.